Friday, October 6, 2017

Tuesday, October 3, 2017

AUREN FANSA CHAPTER 9 & 10

AUREN FANSA CHAPTER 9 & 10

Haka kuwa akayi washe gari da safe Hamza da
Bilki suka fita don saka Meenah a makaranta.
Gobarau Academy itace makarantar da suka nufa,
da zuwansu da komai basu wuce minti talatin ba
aka kammala komai aka saka ta Pre nursery, duba
da shekarunta kuma a k'a'idar makarantar idan
yaro bai kai shekara 3 ba to baza'a saka shi
nursery ba daman. Daman 'yan pre nursery ba'a
saka musu uniform.
A ranar aka barta makaranta kuma ko kuka batayi
ba da su Hamza zasu tafi don ta samu abin wasa
sai dad'i takeji.
K'arfe 12 suke tashi don haka dole Bilki ke d'auko
ta don Hamza na wurin aiki lokacin, ba yadda ta
iya haka nan take hak'ura tana d'auko ta d'in.
Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin hukunci
da hikimar ubangiji, Meenah har ta shiga nursery.
Meenah Allah ya bata k'walwa komai aka koya
mata ta iya sai dai idan ba'a koya mata ba, kuma
idan ta dawo gida ta dinga yi kenan ko gajiya
batayi.
Ba'a saka Zarah makaranta ba sai da Meenah ta
shiga nursery 2 a lokacin ita kuma Zarah tana da
shekara 3 a duniya yayinda Meenah keda hud'u.
Ranar wata juma'a akayi ma su Meenah hutu
suna zuwa gida Meenah ta fara neman babanta
don nuna mai report card nata, sai
dai rashin sa'a yayi tafiya zuwa Lagos a safiyar
ranar, tayi ta kuka tana kiran ita Baba.
Bilki tana tsaki ta ansa report card nata dana
Zarah tana dubawa, abin takaici a wurinta wai
Meenah na d'aya tayi ita kuwa Zarah na ashirin
tayi cikin su ashirin da shidda. Bilki kamar tayi
kuka don takaici. Wato Meenah dai tafi d'iyarta
k'ok'ari kenan?
"Gaskiya da sake!" Ta kalli Meenah tace mata "Ke!
Zo nan!" Meenah tayi tsaye idanunta k'wal hawaye
a duniya tana tsoron Bilki, fizgo ta tayi da k'arfi.
"Ke dan ubanki sai da kika yi na d'aya wannan
karon ma? Kin manta bugun da nayi maki last
term kenan? Salon kija babanta ya dawo ya zane
Zarah ko? Ke ga mai k'ok'ari ko? Shegiya mai
kama da mage! Wuce ki bani wuri!" Da gudu
Meenah tayi d'aki tana kuka sosai, jawo Zarah tayi
ta rungume tace.
"Don Allah d'iyar Baba ki dage kifi waccan
yarinyar k'ok'ari kinji?" Zarah ta gyad'a kai.
Da rana ta zuba ma Zarah abinci ta shiga wanka,
Meenah na zuwa Zarah tace.
"Zo muci." Ba musu ta zauna suka fara cin
abincin tare.
Ba'a jima ba Bilki ta fito wanka tana lek'owa taga
Meenah nacin abin da d'iyarta abinda ta tsana! Da
tsawa tace
"Ke!" A firgice Meenah ta tashi tana kyarma,
Bilki ta k'ara daka mata tsawa.
"Bana hana ki cin abinci tare da Zarah ba?
Shegiya wuce ki tafi d'aki." Tayi d'aki da gudu a
tsorace. Zarah ta aje cokalin hannunta tace
"Bazan ci ba nima sai da Meenah." Daman Bilki
tasan abinda zatace kenan, tsaki taja tace
"To sai dai kar kici wallahi amma bazakici tare da
Meenah ba, kinji na fad'a miki!"
Aikuwa aje cokalin tayi tana fushi sosai ta bar
parlon. Tsaki Bilki ta k'ara yi tana k'ara jin
haushin Meenah...
***
Sauri yakeyi ya dawo gida don nuna ma iyayensa
result nasa na shedar kammala jss3 nasa. Driver
na yin parking ya fito da gudu yana murna
shigarsa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga
masa hankali, ya kuma gigita shi a lokaci guda,
take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri a yayinda
k'walwarsa ta tsaya cak! ta bar aiki lokaci d'aya!!!
Iyayensa ne kwance jina jina, a yayinda wasu
mutane kusan su bakwai ke tsaye cikin bak'ak'en
kaya hartta fuskokinsu an rufe da black mask!
Tsaye yayi ya kasa tantance a wace duniyar yake,
take kuma ya fashe da kuka yana fad'in.
"Su waye ku? Mey...asa ku...ka kashe min
iyaye?"
Direwa yayi k'asa yana kuka yana jijjiga iyayen
nasa a yayinda yake kiran Anisah! Mutumin yayi
dariya yace.
"Ka bar kuka yaro, sun tafi inda ba'a dawowa
kaima kuma yanzu zaka bisu!" Yakece da dariya
sannan ya saita bindigar daodai saitin k'irjinsa ya
harba.
A gigice ya farka duk da Ac d'in da ke aiki amma
hakan bai hana sa yin sharkaf da zufa ba. Ta6a
jikinsa ya soma yi amma baiga jini ba, ajiyar
zuciya ya sauke ya shiga yin addu'a don ba
k'aramin tsoro yaji ba.
"Wane wane irin mafarki ne haka..... ?"
Ya fad'a yana mai k'ara tunawa da mafarkin da
yayi. Zumbur! Kuma ya mik'e ya fice da gudu don
duba lafiyar iyayensa don gani yake kamar da
gaske ne....!
"Mummy...! Mu.." A firgice suka farka daga bacci,
da mamaki suka ce
"Waye?" Kasancewar d'akin gauraye yake da duhu
fitila a kashe take, Daddy ya kai hannunsa ya
kunna bedside lamp yana kallon Faruk dake tsaye,
da sauri Faruk ya rungume mahaifiyar tasa yace.
"Alhamdulillah! Ashe duk lafiyarku lau, wallahi naji
tsoro."
Mummy tayi murmushi don tasan ya k'ara yin
mafarki. Tace
"Faruk nasha fad'a maka mafarki ba gaskiya bane
ka daina d'aga hankalinka akan mafarki, nasha
fad'a maka bakaji."
Faruk yace
"Nasani Mummy amma meyasa a duk lokacin da
nayi mummunan mafarki sai naji gabana ya fad'i,
sannan na kasa samun nutsuwa, gani nake kamar
wani abu na shirin faruwa da mu!"
Daddy yace
"Haba Faruk! Ka zamo mai tawwakali mana, an
fad'a maka mafarki ba gaskiya bane haba! Tashi
kaje ka kwanta."
Sum sum ya tashi ya fice, Daddy ya kalli Reemah
yace.
"Wai shin kuwa yaron nan na addu'a a duk
lokacin da zai kwanta bacci?"
Reemah tace
"Yana yi, kullum sai na je na tabbatar da sai
sunyi addu'a kafin su kwanta su duka."
Daddy ya numfasa yace
"To Allah ya kyauta amma sai ya k'ara dagewa da
addu'a sosai."
Reemah tace
"Insha Allah."
***
BAYAN WATA D'AYA
Zaune yake yana karatu wayarsa ta fara k'ara,
ganin sunan Daddynsa yasa yayi saurin d'agawa.
"Hello kaine Faruk?"
Yace
"Eh nine lafiya ina mai wayar nan?"
"Sai dai kayi hak'uri mai wayar nan ya rasu dashi
da matarsa!"
"What? Innalillahi wa'inna ilahir raj'un!"
"Ya Faruk!"
A firgice ya farka ganin Anisha tsaye gabansa tana
kakkarwa, yasa yace
"Ke lafiya menene?"
Ta fashe da kuka.
"Mummy! Ya Faruk Daddy da Mummy babu."
Yace
"Kamar ya? Ina suke?"
Tace
"Wasu mutane na nan sun zagaye Mummy da
Daddy..."
Kafin ta k'arasa ya mik'e da gudu ya fita."
Zuwansa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga
masa hankali lokaci guda kuma ya gigice ya shiga
rud'ani! Murza idanunsa ya fara yi don yayi
tunanin wannna karon ma mafarki yakeyi, la6ewa
ya shiga yi a bakin k'ofa yana sauraren mutanen
da ke tsaye. Kusan su hud'u majiya k'arfi.
"Hello Hajiya Laila Sunusi! Aikin da kika samu fa
an kammala abu biyu ya rage. Na farko bamuga
yaransu guda biyu da kika lissafa mana ba! Na
biyu takardun gidannan da sauran mahimman
takardun da kika ce a baki."
"Yes Ma! Ok Ma! Insha Allah na miki alk'awarin
cika miki dukkan aikin da kika
samu da ke da aminiyarki ya sunan ta ma? Haha
yes Bilkisu Ringim! Ok..."
Kamo hannun Anisah yayi yana kuka d'akinsa ya
fad'a ya kwashi wasu takardu nasa dashi dana
Anisah na makarantarsa da abubuwan da yake
buk'ata ya jefa jikka suka fito da sauri sukayi
hanyar fita. Anisah na kuka shima yana kuka suka
fito gate, gaba d'aya masu gadinsu basu nan,
security sunfi goma amma yanzu bai ga kowa ba.
Adaidaita ya samu suka wuce wata police station,
yana zuwa ya fad'a masa dukkan abinda ya gani
ya kuma ji sannan yace suzo su ceci iyayensa
kafin su mutu.
Ba 6ata lokaci suka nufo gidan sai dai da
zuwansu abin mamaki ba komai gidan asali ma
gidan a rufe yake da kwad'o sai dai gawar
iyayensa, nan akayi examining d'insu aka tabbatar
da basuda rai, take Faruk ya rasa a wace duniyar
yake, kansa yayi dip, hawaye kuwa kamar an
bud'e pampo. Sambatu kawai yakeyi yana fad'in.
"Daman nasha yin mafarki an kashe mana iyaye!
Nace abin kamar zai faru amma ba wanda ya kula
ni..."
Duk police d'in da yayi yunk'urin tab'asa da
niyyar rarrashi turesu yakeyi suna fad'uwa k'asa,
gaba d'aya kamar ya zauce. Yama k'i nutsuwa
asan ina danginsa suke a sanar masu de abinda
ya faru. Gaba d'aya gidan ba mota ko d'aya,
motocin mahaifinsa sunfi kala takwas amma
yanzu ko d'aya babu.
Nan kuma kan Faruk ya fara juyawa kafin ya
ankara ya fad'i k'asa tim!

Sunday, October 1, 2017

AUREN FANSA CHAPTER 7 & 8

AUREN FANSA CHAPTER 7 & 8

Fatima Zarah fara ce tas sa6anin Meenah da take
ba fara ba tas, murna a wurin Bilki ba'a magana
don yanzu gani take wata sabuwar dama ce ta
samu ta yadda zata dinga samun kud'i a hannun
Alhaji ba tare da wani matsala ba.
Kulawa ta musamman take samu a wurin
mahaifiyarta wadda takeji kamar ta had'iye don
so. A idon Alhaji kuwa had'awa takeyi da Meenah
tana kulawa dasu wanda bata gajiya, bayan
idonsa kuwa Meenah bata samun wata kulawa,
tun daga kan wanka, chanza pampers, cin
abincinta, chanza kaya idan sun 6aci sam bata
damu ba. Sai Alhaji ya kusa dawowa take tashi
tayi mata wanka ta bata abinci yadda komai
tsiyarshi baya ganewa. Zarah kuwa sai ayi mata
wanka sau uku, abinci kuwa duk bayan awa uku
ake bata, sheyasa tun kafin suyi arba'in ta takura
tayi k'iba tayi fam, kamar balloon.
Watan Zarah biyu a duniya Meenah ta shekara
d'aya cas. Tayi kyau tayi wayau abinta. Gata ta
iya magana ba abinda bata fad'i kai kace 'yar
shekara uku. Yadda ta taso ta d'auka Bilki ce
mahaifiyar haka ma Alhaji ne babanta sai dai tafi
shak'uwa da Alhaji saboda muddin yana gida to
suna tare. Sheyasa yanzu idan zai fita sai da
wayau saboda ta dinga kuka kenan kamar zata
sik'e.
***
Ranar wata juma'a Alhaji ya dawo fuskarsa a
cinkushe daga gani yana cikin damuwa, yana
shigowa gaban Bilki ya yanke ya fad'i dama da
safe ya fad'a mata ana neman sa banki don haka
tana ta murna don tasan mijinta ya zama manager
na banki. Yana fita ta hau gyaran gida tayi ma su
Zarah wanka tayi masu kwalliya sosai. Ta shirya
abinci mai rai da lafiya kafin k'arfe d'aya ta gama
komai tana zaman jiransa ya dawo.
Yana shigowa ta tare sa daga bakin k'ofa tana ta
murna kamar zata shige cikin jikinshi. Sai dai kula
da yanayinsa ya sanya jikinta yin sanyi lak'was.
Bayan sun zauna ta fara tambayarsa.
"Alhaji wai ya ake ciki ne? Baka ce komai bafa."
Ya kalle ta na 'yan second kad'an kafin ya
numfasa yace
"Bani akaba ba abokin aikina aka ba."
Dafe k'irji tayi tare da zaro idanu waje. Tace
"Me kace? Kana nufin basu baka ba? Haba !
Gaskiya ba'ayi adalci ba sam."
Yayi murmushi
"Bilkisu kenan, ni banga abin d'aga hankali a nan
ba, kar ki manta komai na duniya rabo ne, idan
bakada rabo komin yadda kakeson abu bazaka
same shi ba."
Shiru tayi tana ayyanawa a ranta. "To wa aka ba?"
Ta tambayi kanta.
"Alhaji Adam Ishaq." Aka ba.
Tashi tayi tsaye
"Haba yanzu kayi magana, ay daman na dad'e da
sanin sun fison su ba Adam, saboda shi yafika
kud'i ko?"
"Haba Bilki! Bana son tashin hankali tunda an riga
an bashi kina da yadda zakiyi ne? Ni ban damu
ba kuma na taya sa murna nima idan lokacin
nawa yazo zan samu. Alhaji Adam mutumin kirki
ne, kuma muna mutunci dashi don haka na taya
sa murna sosai, ke kuma idan na k'ara jin
maganar nan kin tada ita a bakin aurenki!"
Dole taja bakinta tayi shiru, amma tana nan tana
jira ya fita ta kira aminiyarta Hajiya Laila ta fad'a
mata wannan mummunan labarin.
Aiko ana gama sallar magriba ya fice daga gidan,
yana fita ta kira k'awarta Laila tana d'auka Bilki
tac ce
"Wai bakisan meya faru damu ba ko?"
Hajiya Laila cikin d'aga murya tace
"Meyafaru?"
Nan Bilki ta kwashi komai ta fad'a mata tana
gama magana Laila tace
"Ke iya nan kina sani kenan? Tab! Alhaji Adam dai
an amsa transfer zuwa Abuja kiji in fad'a maki,
yayi kud'i abinsa dama kinsan mahashuk'in mai
kud'i ne ba kad'an ba."
Bilki ta zaro idanu waje kamar Laila na ganinta
tace
"Haba ki bari Laila, ta yaya akayi kika sani?"
Laila tayi shewa tace
"Kina nufin baki sani ba? To bari in tak'aice maki
labari Alhaji Adam Ishaq babban d'an kasuwa ne,
sannan yana saida motoci ke kampanin k'era
motoci ke gareshi a k'asashe daban daban.
Bayan nan ga super market da yake dasu ba
iyaka, ga gidajen mai nan tun daga nan Katsina,
Kaduna, Abuja ke babu inda babu. Matarsa ma
shagon saida kayayyaki ke gareta babu abinda
babu k'atuwar mall ce sai dai kin gani."
Bilki da jikinta yayi sannan taji maganar kud'i
yasa tace
"Wai da gaske kike?"
Laila tace
"Ba maganar wasa a nan Hajiya Bilki wallahi
gaskiya na fad'a miki, bakiga kullum basu k'asar
ba? Ke wallahi rayuwarsu abin sha'awa daga shi
sai matarshi sai yaranshi guda biyu kacal ke cin
wannan uban dukiya. Ke suna fantamawa fa.
Kinsan gidanshi dake sabon titin GRA can
wuraren Governor road d'innan ay ko?"
Bilki tace
"Kar dai kice kusa da wannan makarantar premier
boarding school ta mata?"
Laila tace
"Nan fa toh wannan fa, gidanshi nan nan na nisa
sosai, kullum na wuce ta hanyar sai na k'ara
kallon gidan don gidan ya had'u ba kad'an ba."
Bilki tace
"Tabbas na gane gidan, nima ina ganin gidan,
lallai Alhaji Adam ba k'aramin dukiya ya tara
ba..."
Laila tace
"Uhm kedai bari zanzo idan nazo zaki k'arasa jin
sauran bayanan don maganar bata waya bace."
Bilki tace
"Haka ne, gaskiya ina jiranki Laila kar ki shanya
ni."
Laila tayi dariya
"Wallahi zanzo."
"Yaushe to?"
Laila tace
"Zuwa jibi."
Bilki tace
"Ina jiranki."
Daga haka sukayi sallama zuciyar Bilki cike da
tunani kala kala, da kuma sha'awar dukiyar Alhaji
inama ace tata ce, abinda take ta ayyanawa a
ranta kenan.
BAYAN KWANA BIYU
Da safe wuraren k'arfe sha d'aya Laila ta diro
gidan Bilki, aiko murna a wurin Bilki ba'a magana,
nan aka kawo mata kayan motsa baki. Bayan sun
gama gaisawa Laila tace
"Bilkisu mai gadon zinari kenan, yau gani nazo a
gidanki akan labarin da kikeson ji, wato maganar
kud'i."
Bilki tace
"Ina jinki k'awata."
Laila tace
"Ay kamar yadda na fad'a miki rannan toh haka
maganar take, kuma zuwa nan da sati d'aya zasu
tattara su bar garinnan. Niko inada shawara
amma bansani ba ko zaki yarda da ita."
Bilki tace
"Fad'i shawararki."
Laila ta gyara zama bayan ta shanye lemon da ke
cikin glass cup ta soma magana.
"Bilki tunda kinga dani dake duk muna son kud'i
me zai hana mu had'a k'arfi da k'arfi mu k'waci
dukiyar Alhaji Adam."
Bilki ta zaro idanu waje
"Kamar ya? Ban fahimce ki ba."
Laila tayi dariya
"Abinda nake nufi a nan shine, mu had'a k'arfi
nida ke mu k'waci dukiyar Alhaji Adam koda
hakan na nufi mu kashe su."
Da sauri Bilki ta zabura had'e da zaro idanu waje
tana kallon Hajiya Laila...

Laila ce ta cigaba da magana.
"Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?"
Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace
"A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don
ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya mu
chanza shawara dai."
Laila tayi kwafa.
"To sai akace mu zamu bisu mu aikata
k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba, abinda
nake nufi a nan shine..."
Nan naga ta rad'a mata wata magana daga
k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya.
Bilki tana dariya tace
"Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma ke
shu'uma ce wallahi."
Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai sannan
tace
"Kema haka."
Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta tana
kallon Laila tace
"Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta."
Laila tace
"Yi sauri kuwa nima naji."
Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a
hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga
bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara mata
wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama bacci ta
tashi don kuwa kanta buzu buzu yake, saboda
yanayin gashinta mai cika kuma ga tsawo sheyasa
ko ya ta kwanta sai yayi buzu buzu. Zuwa tayi
kusa da Bilki tana murza idanu. Su kuwa sai
faman ta6e baki sukeyi. Meenah tace
"Maama wunwa."
Laila ta ta6e baki tace
"Uban me tace?"
Bilki tace
"Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri."
Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta
matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri
Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim!
"Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila
had'e da jan tsaki.
Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta fashe
da kuka.
Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana
tsaki sannan ta dire mata k'asa.
"Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai
ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan ta
fito daga kitchen d'in.
Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma
Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta
kammala sannan aka bata ruwa.
A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma
Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da
papered chicken sai had'ad'en salad. Wuraren
uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi
gida.
Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma Meenah
wanka ta bata abincin rana.
Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi
wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar fira
kafin a kira sallar magrib. Kasancewar Meenah
batasan dawowar Baban nata ba, tana can d'aki
tana wasa. Sai data fito, aiko tana ganin shi ta
rugo da d'an gudunta ta zo kusa da shi tana
fad'in
"Dada!"
Cike da jin dad'i Alhaji yace
"D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan."
Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa
yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai tace
"Dada kaga Maama ta bije ni d'azu."
Ya ware idanu
"Me kikayi wa Maama ta bige ki?"
Tayi shiru tana kallonsa can tace
"Bakomai."
Bilki ta taso tana dariya tace
"Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga
wanka nazo na iske ta tana zubar da madara,
shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi dariya
"Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko?
Idan Maama tace a daina a daina kinji?"
Ta gyad'a kai. Sai kuma yace
"Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son cin
abinci?"
Tayi dariya tace
"Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da
yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi mamaki
sam batason ci na rasa dalili."
Yace
"To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko
wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba
fad'a zatayi ba."
Tace
"To k'ila dai."
Ya juyo da dubansa ga Meenah
"Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?"
Nan ma shiru. Yayi murmushi
"Zaki sha ice cream?"
Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji
dad'i yace
"Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo
gida zan siyo maki harda biscuit ma."
Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace
"Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi
sai na dawo."
Tace
"A dawo lafiya."
Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da Meenah
dake tsaye a tsorace gaban Bilki.
Tana huci tace
"Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan nan
yake da yarinyar nan amma naga ba ruwanshi ma
da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya a cikinka
amma ka nuna son d'iyar wata? To da sake mts."
Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana
zare idanu.
Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya
tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit sai
ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara. Zarah
kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya siya
mata tunda yasan bata isa shan wad'annan kayan
ba.
Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna, ya
bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye tas
sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki.
Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa
yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi. Bilki
na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah. Can
Alhaji yace
"Ina Meenah tayi ne?"
Tayi tsaki a ranta tace
"Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma tunda
bazata ci abinci ba."
Tashi yayi yana fad'in
"Ina zuwa."
Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah.
Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa da
biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta. Murmushi
yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan gado, ya gyara
mata kwanciya sannan ya kashe fitilar ya fito.
Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta
k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka.
BAYAN KWANA BIYU
Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo,
tana d'auka Laila tafara magana
"Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji
Adam sun koma Abuja gaba d'aya."
Da sauri Bilki tace
"Haba dai? To yanzu ya kenan?"
"Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don
gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji
ne a gidan."
Bilki tace
"Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi
yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara."
"To shikenan." Laila tace tare da katse kiran. Nan
tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita.
***
Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi
shekara d'aya amma har yau sun rasa wata
mafita.
A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda
rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta
makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci
zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta iya
saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta fito ga
surutu ba abinda bata fad'i.
Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don
muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta
fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin
komai har ya fara zarginta...

Saturday, September 30, 2017

AUREN FANSA CHAPTER 5 & 6

AUREN FANSA CHAPTER 5 & 6
BAYAN KWANA BIYU
Ranar suna yarinya taci sunan mamanta
marigayiya Amina, daman bawani taron sunan da
akayi wane taro ma ana zaman makoki?
Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata
hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji yunwa
ko wani abin na damunta. Kammaninta sak na
mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin nata ne
lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba sa6anin
marigayiya da take fara tas kamar yayanta Hamza
amma Amina babyn ita ba fara bace tas, sai dai
tana da kyau duk da batada hasken ana ganin
kyawunta. Idan ta bud'e ido ta kalli mutum zaka
gansu manya ne farare tas!
Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20
cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki gidanta
akan cewa tana son magana dasu.
Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko Amina
dake kwance kan gado tana bacci, ta mik'a ma
Hamza ita tana murmushi tace
"Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka
amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin
haka, don haka yau na damk'a maka Amina a
matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka rik'e
ta bisa amana."
Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace
"Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana
saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya
idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya."
Hamza yace
"Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar
Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a
raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya
taya mu rik'o."
Goggo tace
"Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar
mata a ciki ake siya mata su pampers da su
madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a
rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da kud'in
ba sai idan ba kud'i hannuna, amma tunda yanzu
zata dawo hannunku da zama sheyasa zan
damk'a maka kud'inta a hannunka ka adana mata
ko ka juya mata su duk yadda kaga ya dace."
Jiki a sanyaye Hamza yace
"Insha Allah Goggo."
Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina
tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin mota.
Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma
gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina
sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba
har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar ta
shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi
zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake ransa
ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar Amina kamar
'yar cikinta.
Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a
ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta
shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink
wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi
irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e
yake gwanin kyau.
Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata
tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci,
duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon
mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki
nayi.
Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa
da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta
masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka
sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama
don haka sai ya yafe mata suka shirya.
Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata
tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi
sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta da
kuma an bata madara zata koma shikenan kuma
sai asuba.
Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata
madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin za'a
samu wata matsala ba daga wurin Bilkin ba.
Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da maganar
k'arin aure.
Duk sadda Hamza ke gida to Amina na hannunsa
yana mata wasa, yana ce mata
"Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata
pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta har
sai tayi bacci.
A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah
yake ce mata idan yana mata wasa.
Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin
k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta, ga
bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai dad'a
kyau takeyi kullum.
Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum
yana manne da ita especially weekends ranar da
ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana
kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata
daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba,
tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta taso
cikin ingatacciyar rayuwa.
Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki,
Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna
had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi.
Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun
cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar
hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan
lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa
bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje da
yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba sheyasa
bai farga ba, sai dai idan yaga kamar kud'in ba
daidai suke ba yayi ta tunanin yadda akayi ya
kashe su.
***
Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi ruf
da ciki yana game cikin system d'insa. Sai yanzu
na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in d'akin
dark da light blue ne, hartta gadonsa blue ne da
bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama. Carpet
d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne. Gefe guda
kuma study table ne shima blue, sai cikin wata
k'atuwar box kayan wasansa ne wanda mafi yawa
nafi hango jirgin wasa kala kala, hartta kan
gadonsa jirgin wasa ne yakai biyar gefensa, d'aya
kuma a hannunsa, a raina nace to shi kuma son
jirgi yake?
Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin
kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta
dafa shi.
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace.
"Mummy na."
Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan
tace
"Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka koyi
hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a islamiyya?"
Murmushi yayi yace
"Nayi Mummy."
Tace
"Anya Faruk?"
Yace
"Allah yanzu na gama."
Tace
"Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta
'yar shekara uku) suna jiranmu."
"Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi
bayan Mummy....
Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke
zaune suna labari harda dariya, zama sukayi itada
Faruk
da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta zuba
ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit sai
k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun ta
hanyar jefo ma Daddy tambaya.
"Daddy idan na girma me zan zama?"
Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata
yana kallon Anisah kafin kuma yace
"Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama
ay."
Anisah tayi dariya
"Ni banason na zama komai nafiso na shiga
aljanna."
Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta
kafin kuma Mummy tace
"Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?"
Mummy tace
"Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko sun
fasa?"
Daddy yayi murmushi
"Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba
cancanta kafin su bada, idan na dace a bani
manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a ba
za'a bashi."
Tayi murmushi
"Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a a
dukkan lamuranka"
Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba, abinda
ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin yi masa
addu'a takeyi yana murmushi yace
"Amin ya Allah Reemah."
"Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in
kuwa?"
Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake
bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin
yace
"Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su
Faruk sun gama exams a islamiyya."
"Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?"
Mummy tayi murmushi tace
"Eh Mamana ko bazaki ba?"
Anisah ta zum6ura baki
"O'o ni zanje."
Faruk yace
"Kalle ta to baza'a dake ba."
Anisha ta sa kuka
"Daddy wai baza'a je dani ba?"
Daddy yayi murmushi
"Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar
gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu
iya barinki ba."
Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk
yasa dariya. Anisah tasa kuka.
"Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?"
Mummy ta harari Faruk
"Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin
kukan k'anwarka ne?"
Yayi dariya
"Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata
hak'uri ba?''
Ya buga k'afa.
"Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab bazan
bada ba."
Daddy yace
"Just say sorry Faruk, you know she won't stop
crying unless you apologize."
Mummy tace
"Oya Faruk now!"
"Ok sorry!"
Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin
abincinta kafin kuma ta kalli Daddy
"Daddy zansha ice cream."
Mummy tace
"Me nace miki akan zak'i?"
Anisah ta turo baki
"O'o ni zansha."
Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga mata
hannu
"Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream."
Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana
tsallen dad'i.
Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace
"Anisah kenan, badai rigima ba."
Daddy yayi dariya
"Lokacinta ne, kema kinyi naki ay."
Mummy tace
"Daddy Faruk fa na wurin."
Yayi dariya
"To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay"
Da sauri ta tashi tana fad'in
"Haba Daddy!"
Yayi dariya
"Kina tantama ne? Bari kiga..."
Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya.
Daddy ya tashi ya bi bayanta
"Guduwa kikayi Reemah!"
Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin
ransa yace
"Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely family!"
***
Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin
wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki
dake zaune saman kujera tana shan rake tana
kallon wani movie da take so kukan Meenah ya
cika mata kunne. Tsawa ta daka mata
"Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen
kuka haba!"
Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata
ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani irin
kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi
shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman
kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka baiwar
Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa tayi ta ajiyar
zuciya har baccin wahala ya kwashe ta a nan.
Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar
motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki
Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da zama
kan kujera tana rirriga ta.
Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi a
saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki ta
kalle shi
"Sannu da zuwa Alhaji."
Yana murmushi yace
"Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?"
Tayi murmushi
"Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga ta
tayi bacci."
Yayi murmushi
"Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai
baccin takeji daman."
Tayi yak'e
"Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada
rigima."
Yace
"Hakane Allah ya raya mana ita."
Tace
"Amin."
Yace
"Bari naje na watsa ruwa na gaji."
Tace
"Ok sai ka fito."
Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja dogon
tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a d'akin
Meenah d'in kan gado.
Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan
dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace
"Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai nace
Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar da
kikeyi. Allah ya baki lada."
Ta kalli Alhaji tace
"Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine, kuma
ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka na
d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji
kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina ba."
Yayi murmushin jin dad'i
"Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na yaba
da k'ok'arinki."
Tayi dariya
"Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da
pampers sun k'are shine nace ya kamata a bad a
siyo mata wasu."
Yace
"Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki
siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison
madarar ma akan abinci."
Tace
"Hakane."
Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma
ya bata. Amsa tayi tace
"Shikenan zanje na siyo mata.
Yace
"Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana."
Da sauri tace
"Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake gida
kullum ka bari zan siyo mata."
Yayi murmushi
"Toh shikenan."
***
Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta
tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba
saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu.
Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan,
Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba ta
haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai k'oshin
lafiya.
Haka aka cigaba da zaman barka inda komai
Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana
tafiya daidai.
Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin
Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna
aka watse lafiya kowa ya koma gidansa....

Friday, September 29, 2017

AUREN FANSA CHAPTER 3 & 4

AUREN FANSA CHAPTER 3 & 4
Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da
maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi
6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna
mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya
dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya
amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma
cikin d'aki tsabar borin kunya.
Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe
idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin
hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in
wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My
sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a
lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka
yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka
amsa sannan tace.
"Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?"
Sai da yayi murmushi sannan yace
"Lafiya lau Amina ya gida?"
"Alhamdulillah, ya Anty Bilki?"
"Tana nan lafiya ya zafi kuma?"
"Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?"
Yace
"Alhamdulillah ya jiki kuma?"
Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace
"Alhamdulillah gashi nan muna ta fama."
Dariya yayi yace
"To Allah ya raba lafiya."
Tace
"Amin."
Sannan ta kuma cewa
"Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira
ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa
kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan
na baka shi ka rik'a..."
"Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai
ki dinga kawo min shi hutu."
Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace
"Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi
min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan
raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu."
Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici
yace
"Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne
kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har ma
ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu haka
ba dad'in ji."
Tayi dariya
"Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu
sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?"
Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora
"Naji shikenan are you happy now?"
"Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!"
Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann ya
kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata
tambaya
"Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike
buk'ata?"
Tace
"Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na
bata."
Yace
"Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a
siya."
Tace
"Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i."
Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi
sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da
d'an uwanshi.
Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya,
bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa
bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi
Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan ta
haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa
suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina
kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna
tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba
su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya.
Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta
da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure
ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba.
Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah
ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba
haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa,
bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke
cikin garin Katsina a G.R.A.
Wannan kenan!
***
BAYAN 'YAN KWANAKI
Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka
yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da
Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita
unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A
hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke
su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky
doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an
mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta
yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini
ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta
zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki
tace.
"Hamza zan fita."
Ya kalleta da mamaki yace
"Ina zakije?"
Ta had'e rai
"Gidan Hajiya Laila."
Shima ya had'e rai
"Ba inda zakije."
Ta mik'e zumbur!
"Me kace?"
Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa
masifa
"Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai! Kuma
ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta taka
duk ta zuge ka."
Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa
"Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu
saboda babu ruwanta, kina ji na?"
"Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an
fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi."
Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace
"Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki
wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in
magana makamancin wannan a bakin aurenki!"
Ta zaro idanu waje
"Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu kayi
baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i gaskiya
shikenan kaje Allah zai saka min."
Yace
"Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita
bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To
mugani idan kin isa!"
Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo.
"Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara
na gaji da zama da mace irinki wadda batasan
inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina
tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure."
A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura
taga nama.
"Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni
kad'ai ce babu k'ari!"
Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on
da tayi masa sannan yace
"Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar
anyi ne an gama."
Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko
kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in
"Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta
zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe
ta!!!"
Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi
kan gadonsa yana mai maida numfashi sama
sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta
ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri
iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam
bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren
su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki
bata yi mata ba, batada kamun kai ga shegen
yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta
baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a
Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai
iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya
hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da
yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji
kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka
yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya
ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya
kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana
tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an
zata sa masa kuka.
Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya
yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila
hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin,
wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki
ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da
niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya
ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara
ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar
haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya
d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace
"Hamza kana ina yanzu?"
Yace
"Ina gida Goggo, lafiya dai ko?"
Tace
"Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti
k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe tak'i
shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga
haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza,
kayi sauri don Allah."
A rud'e yace
"Gani nan yanzu wace asibiti ce?"
Tace
"Alheri clinic kayi sauri."
"To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin,
takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga
gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya
figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada
nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da
sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso
Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar
suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya
kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa.
Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo.
Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda
takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka.
Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin
kuka tana fad'in
"Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan
fad'a maka."
Jikinsa yayi sanyi yace
"Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..."
"Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na
haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!"
Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara
safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan
tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan
maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce
zata fad'a masa. Don haka sai yace
"Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki
tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan."
Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar
k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da
malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take
"Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min
alk'awari na k'arshe."
Da sauri ya kalleta
"Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun
gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado
zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana."
Girgiza kanta tayi tana hawaye
"Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin
kawai."
Goggo ce ta sa baki tace
"Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata
alk'awarin a shiga da ita."
Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace
"Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki
lafiya."
Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata
yin mumushi ba, sannan tace
"Nagode ya Hamza nagode!"
Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin
Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da
Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu
aka raba su da k'yar."
Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina
bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya
dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru.
Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa
haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da
k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara
shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin
ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri
suka fara murna suna hamdala.
Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa
su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa
"Alhamdulillah! Ta haihu lafiya."
Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana
kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana
murmushi sosai. Nurse d'in ce tace
"Ta haifi mace."
"Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa.
Kafin kuma Goggo tace
"Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu
shiga?"
Nurse d'in ce tace
"Sai dai kuyi hak'uri..."
"Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an
rud'e, Goggo ma ta rud'e tace
"Bamu gane abinda kike cewa ba."
Nurse d'in tace
"Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya
amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga
mahaliccinmu."
Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse
d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda
salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta
sukayi ta zauna da sauri.
Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin
kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro.
"Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a
min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta
sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke
kuka rungume da babyn.
Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin
farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin
kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma
rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon
yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye
tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka
6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin
doguwar ambulance.
Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin
gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi.
Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa.
Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida.
Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai
kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na
k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani
ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina
tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin
sakata a makwancinta.
Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su
Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa.
Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo
komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma
sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata
damuwa ba.
A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki,
inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar
kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya
k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko
kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana
kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar.
Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar
k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin
wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace,
Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin
thumma Amin.

Wednesday, September 27, 2017

KWANA TARA NA BARAWO LABARI CIKIN HOTUNA

 KWANA___TARA___NA___BARAWO
 LABARI CIKIN HOTUNA
Rundunar 'yan sanda ta Najeriya tayi nasarar kame wasu manya manyan' yan fashi da makami , gamida masu garkuwa da mutane akan hanyar Kaduna zuwa Abuja , dakuma hanyar Abuja zuwa Lokoja , da Abuja zuwa Nasarawa
Wasu daga cikin 'yan fashin dai suna sanye da kaki irin na sojojin Najeriya , kuma dauke da manyan makamai a hannunsu
' Yan jaridu dai sun samu daman tattaunawa da wasu daga cikinsu domin karin bayani
Wani me suna  USAINI ya shaidama manema labarai cewa lallai talaucine ya jefashi cikin wannan mummunan aika-aika , da aka tambayeshi a ina suke samun kayan jam'an tsaro da suke amfani dashi sai yace wai idan sunyi fashi ne suke samu acikin jakukkuna da suka kwata
Rundunar tsaron ta 'yan sanda dai sunyi nasarane bayan sun fafata da wadannan gaggan baryi ne inda jami'an tsaron sukai nasarar harbe mutum bayar daga cikin' yan fashin har lahira , kuma sukai nasarar kama dayawa daga cikin batagarin mutanen
Wannan nasarar da UBANGIJI ya baiwa jami'an tsaron dai yanada nasaba da irin jajircewar da wannan gwamnati me albarka ta baba  BUHARI ke yi wajen ganin ta yaki ta'addanci da 'yan ta'adda a lungu da sako na kasarmu Najeriya harma da makwabta
Daga karshe muna rokon ALLAH da ya kara tona ma duk wani azzalumi da azzalumai asiri a wannan kasa tamu Najeriya , su kuma jami'an tsaro UBANGIJI ya kara musu juriya da basira wajen jajircewa akan aikinsu na tsaron kasa da al'ummarta .

AUREN FANSA CHAPTER 1 & 2



Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin
mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda
zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka,
don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma
tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka
fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga
bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar
tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa
cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye
6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har
yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance
tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin
wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da
takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar
kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah
ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki
wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma
zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta
tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye
bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana
cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain
nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya
za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure
amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa
ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke
gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin
ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan
gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni
ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata
mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse
idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa,
tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma
yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin
haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin
kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba
Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai
hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce
sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi
dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai
kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya
baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har
akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa
da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya
cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki
idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai
baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata
yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa
sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba
tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi.
Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o,
kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta
ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na
manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa
nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe
amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya
kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake
Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi
murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta
gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga
d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.
D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa
ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen,
fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor
ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar
Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan
ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci
guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci
ya sace sa.
Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da
ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm,
zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah,
bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin
Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya,
kiranta yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi
k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana
fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har
lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi
sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na
gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama
mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya
shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar
nauyi ya fice daga gidan.
Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan
Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana
shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba
bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon
masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi
ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar
kullum sannan ta soko masa zancen da kullum
baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana
son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin
hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa
dai na k'asa.
"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma
ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana
buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan
kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma
bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma
mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin
Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole
yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan
zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare,
gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce
d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito
parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani
American series, jin alamun shigowa yasa ta
kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera
yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi
kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa.
Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse
shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce
tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da
shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro
kaya."
Shiruyayi gami da sauke nannauyan numfashi
yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun
rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai
kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma
bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa
basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi
don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in
nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai
na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana,
ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi
kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan
don ya fusata.
Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya
tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa
tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya
jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce
yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata
zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh"
sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza
kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai
lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office
d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji
yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar
kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a
ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku
dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice
tare da sauran abokanan aikinsa musulmai.
Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro
gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa
data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa
taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai
k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana
mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a
hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa
kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor
ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen
don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da
cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan
dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a
kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da
kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine
nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen
wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka
huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don
yaga lokacin sallar magriba ta gabato.
***
"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya
rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin
makekiyar kujera tana duba magazine da glass
d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta
kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa
cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging
d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin
murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum
dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa
harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar
da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana
murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya
lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake
tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk
sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka
basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi
k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka
ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa
da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar
kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya
zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo
muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah
wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara
mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya
fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo
hannun mutumin tayi mai suna Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara
fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi
kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna...

Tofa gawata sabuwa mutanan Nigeria

Don Allah A Ba Ni Amsar Wadannan Tambayoyin

Daga Hajiya Jamila Moh'd Mataimaki

Wai a ma'aikatun, CBN, NNPC, Kwastan, EFCC da sauran manyan ma'aikatun gwamnati ba a daukar sabbin ma'aikata ne da ba za a sanarwa da 'ya'yan talakawa su jaraba sa'a ba?

Me ya sa sai a bangaren aiyukan wahala ko na saida rai ko wanda babu wani albashi mai tsoka a cikin sa, kamar su soja, dan sanda, malamin makaranta da sauransu sannan za a sanar da 'ya'yan talakawa su je su nema?